Mace Duniya Ce. (The Woman is The World), By Maryam Umar Sokoto

Mace Duniya Ce. The Woman is The World.

Macen Arewa kin zauna a durkushe, kafafunki zasu yi sanyi ko kuma ki samu nakasa.
Mike da tsaye tamkar isashshiyar bishiyar giginya da hawanki zai kasance sai an shirya.
Gidan aurenki shine duniyarki, lalacewarta ko jin dadinta ya na tafin hannunki, idan kin so kiyi fatali ki rungume bakin ciki idan kuma kin so ki kirkiri farin ciki ki bayar da farin ciki.

Ba wanda zai so ki tamkar yadda zaki so kanki, ashe kuwa idan kika saka farin cikinki akan sahun farko bana tunanin bakin cikin wani da namiji yayi ajalin rayuwarki ko ke ki kasance mutuwarsa.

Ke tamkar danyar bishiya ce mai yalwataccen ganye, idan aka tsigeki manema inuwarki zasu tozalta, idan suka sassaki bawanki zasu kasance cikin kwararren baya.

Darajarki itace bangon darajarsu, su watsar su ragwanta su mutuntaki su rabauta.

Ilminki shine saninsu, su barki da jahilci su dulmiya cikin duhu, su ilmantaki su samu haske a gidajensu.

Babu bukatar ki roki taimakonsu domin kuwa kin kasance jin dadinsu, su ni’imtar dake ki rahamce su, su matse miki lamba su koka da hawayenssu.

Ko kun san cewar farin cikin namiji yakan tsaya ne akan farin cikin matarsa, shi kuwa farin cikin mace ya kan yalwanta ya lullube duniya da ababen da suke cikinta? Meyasa ba zaku wajabta farantawa matanku ba? Me yasa kuke tunanin su lankwasshin awaza ne da ba zasu amfaneku ba? Me yasa kuke tunanin ilminta ya takaita tsakanin madafa zuwa dakin bacci ne? Shin ba ita bace tushenku ba? Ko kuna tunanin fitowa daga mummunan tushe zai kyautata rayuwarku?

Ku kyautatawa matayenku, sun kasance ababe mafi darajar da suke dauke da darajojinku.

Ku ilmantar, ku faranta mata, ku kyautata mata ku jiyar da ita hutu sao duniyarku ta kyautata, hannayenku su kasance na gwal komai kuka taba zai yi alkali.

Mace Duniya ce.

 

The woman is the world.

A Northern Woman you sit on your knees, your legs will get cold or you will get deformed.
Stand up like a big palm tree and your climb will be ready.
Your marriage is your world, its destruction or pleasure is in your palm, if you want to embrace sadness if you want to create happiness give happiness.

No one wants you as much as you love yourself, but if you put your happiness first, I don’t think of anyone’s grief over the death of a man or your death.

You are like a green tree with many leaves, when your shade is cut off your shadows will fall, and if they cut your servant they will be in a professional back.

Your dignity is the wall of their dignity, they are abandoned, weakened, humane and successful.

Your knowledge is their knowledge, let them sleep in ignorance to immerse themselves in darkness, let them learn to shine in their homes.

You do not need to ask for their help because you are their comfort, their kindness, their pressure, and their tears.

Did you know that a man’s happiness depends on his wife’s happiness, and a woman’s happiness is based on the abundance of the world and its contents? Why not make it compulsory for your wives to please? Why do you think they are so boring that they will not benefit you? Why do you think her knowledge is limited between the kitchen to the bedroom? Isn’t that your source? Do you think getting out of a bad environment will improve your life?

Be kind to your wives, they are the most precious things in your life.

Educate her, please her, treat her well and make her a holiday so that your world will be better, your hands will be golden and everything you touch will shine.

*A woman is a World*

A Northern woman lives bowing, you will cold shoulder yourself or else demean yourself vulnerably.
Stand up like a satisfied celeb palm tree that can not be climbed up easily, but with preparedness.

Your matrimonial house is indeed your world. Your misfortune and even comfortability lay in your hands if you wish to throw your fortunate away and embrace a mishap, if you wish, you may create lasting happiness at your home.

Nobody will admire you like yourself, therefore if you provide yourself with comfortability, no doubt you will be in the frontline of those women who tactically escaped the molestation from their male counterparts that will result in either your death or his own.

The woman is the world.

translated by Mallam Abubakar M. Shehu and Mr. Yusuf

Biography

Maryam Umar Sokoto
I am from Sokoto
Studying Law at Usman Dan Fodio University
I’m a Hausa Novel writer and a Poet.

The winner of the BBC Hausa Short Story Writing Competition on Covid-19.

20-year-old Maryam wins

BBC Hausa, Maryan wins 2020 Writing competition

 

Share

This Post Has One Comment

  1. Patricia

    I have read several good stuff here. Certainly value bookmarking for revisiting.
    I surprise how a lot attempt you set to create this type of fantastic informative web site.

Leave a Reply